5 Nuwamba 2019 - 04:41
Iran Za ta Harba Taurarin Dan Adam Guda 3 Nan Da Wasu Shekaru

Iran Za ta Harba Taurarin Dan Adam Guda 3 Nan Da Wasu Shekaru

(ABNA24.com) Shugaban hukumar kula da sararin samaniya na kasar Irankuma mataimakin ministan sadarwa na kasar Murtaza Barari ya bayyana cewa wannan yana karkashin ci gaba da mataken daI take dauka na kara habaka harkokin da suka shafi sararin samaniya a kasar. Yanzu haka akwai taurarin dan Adama guda 3 da ake ci gaba da aiki akansukuma ana sa ran nan da wasu shekaru masu zuwa za’a aikasu zuwa sararin samaniya.

Ya ci gaba da cewa Iran ta kaddamar da shirin kara bunkasa ayyukan da suka shafi sararin samaniya zango na biyu ne a shekarta ta 2016kuma za’ta ci gaba da samar da abubuwan da suka shafi sararin samaniya har zuwa shekata ta 2025.

Har ila yau ya jaddada cewa ya zuwa yanzu babu wata kasa da ta taimakawa Iranwajen bunkasa tauraron dan Adamdin da ta harba. Ya kuma kara da cewa manyan jamio’in Iran sun taka muhimmiyar rawa wajen samar da kyakkyawan tsari na dogon lokacin a wannan fanni.

Daga karshe ya fadi cewa tauraron dan Adam na farko kirar cikin gida daIran ta harba sararin samaniya mai suna Omid wato Fata a shekara ta 2009 an yi shi cikin nasara, inda ya aiko da bayanai da hakan ya kara karfin guiwa sosai ga kwararrun kasar.



/129