4 Nuwamba 2019 - 09:03
Ana Gudanar Da Zanga-Zangar Ranar Yaki Da GirmanKai Na Duniya A Fadin Kasar Iran.

Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan alummar kasar Iran ne suke jerin gwano a fadin kasar domin tunawa da ranar 13 ga watan “Aban” wato ranar yaki da masu girman kai na Duniya, mai taken , gwagwarmyar musulunci da kasashe ma’a bota girman kai na duniyaa matsayin kafa dan ba na rushewar kasar Amurka.

(ABNA24.com) Rahotanni sun bayyana cewa dubun dubatan alummar kasar Iran ne suke jerin gwano a fadin kasar domin tunawa da ranar 13 ga watan “Aban” wato ranar yaki da masu girman kai na Duniya, mai taken , gwagwarmyar musulunci da kasashe ma’a bota girman kai na duniyaa matsayin kafa dan ba na rushewar kasar Amurka.

Jerin gwanon na yau an fara shi ne daga shekar lekan asiri wato ofishin jakadancin Amurka dake nan birnin Tehran da aka kwace, inda dubban mutane da suka hada da daliban makaranta da na jami’oi suka halarta.

Majalisar tuntutuba ta yada koyarwar addinin musulunci a yankin Khuzistan na kasar Iarn ta fitar da wata sanarwa da a ciki take cewa dubun dubatan alummar lardin suke bi sahun takwarorinsu na sauran jihohi na tunawa da ranar yaki da masu girman kai na duniya da kumaranar da aka tura wanda ya kafa jamhuriyar musulunci ta Iran Imam Khumaini zuwa gudun hijira kasar Turkiya.

Taken wannan shekara kamar yadda jagoran juyin muslunci Ayyatulah Sayyid Khamina’I ya bayyana, gwagwarmaya da kasashe ma’abota girman kai mafarin rushewar Amurka.



/129