(ABNA24.com) Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; dukkanin takunkuman da Amurka take cewa ta kakaba wa Iran a halin yanzu duk maimaici ne.
A lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai yau a birnin Tehran, Sayyid Abbas Musawi kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa, Amurka ta riga ta kai makura kan duk wani takunkumi da za ta iya kakaba wa kasar Iran a halin yanzu.
Ya ce a lokacin da Amurka ta fifita yin amfani da ta’addancin tattalin arziki a kan diflomasiyya a mu’amalarta da Iran saboda ‘yancin siyasa da kasar take da shi, da kin amincewa ta zama ‘yar amshin shata, wannan ba zai taba sanya kasar Iran ta mika wuya ba, bil hasali ma hakan ne ke kara sanya ta jajircewa da kara yin himma wajen dogaro da kanta.
Sayyid abbas Musawi ya ce; dukkanin takunkuman da Amurka take ta ikirarin cewa cewa ta kakaba wa Iran har ma da na baya-bayan nan a kan kayayyakin gine-gine duk maimaici ne, ba wani sabon takunkumi ba ne.
Ya ce maimakon haka tun a hlin yanzu Amurka ta rasa wani abu da ya rage wanda za ta kakaba wa Iran takunkumin a kansa, da zai fi kyau gare ta, ta koma cikin yarjejeniyar shirin Iran na nukiliya domin kare mutunci.
/129
3 Nuwamba 2019 - 05:43
Lambar labari: 985711
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa; dukkanin takunkuman da Amurka take cewa ta kakaba wa Iran a halin yanzu duk maimaici ne.