16 Oktoba 2019 - 04:34
Sojojin Siriya Sun Karbe Ikon Birnin Manbij

Sojojin gwamnatin Siriya, sun kwace ikon gabadayen birnin Manbij da kewayensa, a kokarin da suke na hana birnin fadawa hannun sojojin Turkiyya.

(ABNA24.com) Sojojin gwamnatin Siriya, sun kwace ikon gabadayen birnin Manbij da kewayensa, a kokarin da suke na hana birnin fadawa hannun sojojin Turkiyya.

Wannan na a cikin yarjejeniyar da aka cimma tsakanin sojojin gwamnatin Siriyar da kuma mayakan Kurdawa, wandanda suka nemi agaji daga gwamnatin Siriya akan keta hurumin kasar da Turkiyya ta yi na kaddamar farmaki kan Kurdawan na (YPG), da take dangantawa da ‘yan ta’adda.

A yayin da ake nuna fargaba akan halin da ake ciki, na yiyuwar barkewar wani sabon tashin hankali tsakanin Siriya da Turkiyya, kasar Rasha ta ce ba za ta taba bari a kai ga fada ba tsakanin a tsakanin sojojin Turkiyya da kuma na Siriya ba, kamar yadda wakilin musamman na Rasha, Alexandre Lavrentiev, ya sanar.

Tun dai bayan da Turkiyya fa kaddamar da farmaki a arewacin kasar ta Siriya, kimanin mutane arba’in ne suka rasa rayukansu, kana wasu 165 suka samu munanen raunuka, a yayin da rikicin ya tilasta wa mutane 190,000 yin gudun hijira kamar yadda kungiyar bayar da agaji ta red crescent ta sanar.



/129