(ABNA24.com) Rahotanni daga Aljeriya na cewa, daliban jami’a sun gudanar da zanga zanga yau Talata a Algers babban birnin kasar, duk da jami’an tsaron da aka jibge.
Wannan ita ce ranar Talata, ta 34 da daliban jamia’ar kasar ke gudanar da zanga zangar kin jinin gwamnatin kasar.
An dai kamala zanga zangar ba tare da samun wata mastala ba.
Masu zanga zangar dai na ci gaba da nuna kin jinin shirin gwamnatin kasar na gudanar da zabe, a ranar 12 ga watan Disamba na wannan shekara.
Haka kuma suna ci gaba da kira ga manyan jami’an kasar wadanda suke wa kallo a matsayin na hannun daman tsohon shugaban kasa akan su ma suyi murabus, ta yadda za’a gudanar da sahihin zabe.
/129