13 Oktoba 2019 - 04:44
Jamus Ta Dakatar Da Mika Wa Turkiyya Makamai

Kasar Jamus ta sanar da dakatar da mikawa kasar Turkiyya makamman yaki wandada ta ce kasar ta Turkiyy na iya amfani dasu kan Kurdawa a arewa maso gabashin Siriya.

(ABNA24.com) Kasar Jamus ta sanar da dakatar da mikawa kasar Turkiyya makamman yaki wandada ta ce kasar ta Turkiyy na iya amfani dasu kan Kurdawa a arewa maso gabashin Siriya.

A wata hira mujjalar Bild, ministan harkoin wajen kasar ta Jamus, Heiko Maas, ya ce, kasarsa ta dakatar da mika wa Turkiyya makamai a daidai lokacin da Turkiyyar ke kai farmakin soji a arewa maso gabashin Siriya.

Matakin a cewar Mista Maas, ya shafi dakatar da baiwa Turkiyya duk wani lasisi na kayan soji wandanda Turkiyyar kan amfani dasu a Siriya.

Saidai ministan harkokin wajen na Jamus bai fayyace ko wadanne irin makamman yaki ne ba ko kuma kudadensu.

A baya bayan nan dai manyan kasashen duniya, da dama sunyi tir da matakin sojin da Turkiyya ta dauka kan kurdawan a arewa maso gabashin Siriya,wadanda take dangantawa da alaka da kungiyar PKK da mahukuntan Turkiyya ke kallo a matsayin ‘yan ta’adda.



/129