7 Oktoba 2019 - 05:33
Ana Zaben ‘yan majalisar dokoki a Tunisia

A Tunisia, yau al’umma ke kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.‘yan takara sama da 15,000 ne ke fafatawa a zaben domin samun wakilci a a kujeru 217 da majalisar dokokin kasar ta kunsa.

(ABNA24.com) A Tunisia, yau al’umma ke kada kuri’a a zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.‘yan takara sama da 15,000 ne ke fafatawa a zaben domin samun wakilci a a kujeru 217 da majalisar dokokin kasar ta kunsa.

Zaben dai na zuwa ne bayan na shugaban kasa zagaye na farko da aka gudanar, bayan rasuwar shugaban kasar Beji caib Essebsi a watan Yuli day a gabata.

Jan aikin dake gaban ‘yan takaran da za’a zaba shi ne farfado da tattalin arzikin kasar dake tangal-tangal.


/129