(ABNA24.com) Rahotanni daga Iraki na cewa mutane 60 ne suka rasa rayukansu da suka hada da 18 a Bagadaza, tun bayan barkewar zanga zanga a kasar a ranar Talata data gabata.
Wasu alkalumma daga majiyoyin gwamnati da kamfanin dilancin labaren AFP, ya fitar sun kuma nuna cewa akwai daruruwan mutane da suka samu raunuka.
A ranar Talata data gabata ce aka fara zanga zangar data samo asali daga shafukan sada zumunta, akan cin hanci da rashawa da rashin aiki.
Rahotanni daga kasar sun ce ko a jiya Juma’a ma an sha artabu tsakanin jami’an tsaro da masu zanga zangar, duk da dokar ta bacin da aka kafa, da kuam katse hanyoyin sadarwa na intanet.
/129
6 Oktoba 2019 - 06:02
Lambar labari: 980529
Rahotanni daga Iraki na cewa mutane 60 ne suka rasa rayukansu da suka hada da 18 a Bagadaza, tun bayan barkewar zanga zanga a kasar a ranar Talata data gabata.