(ABNA24.com) Wakilin Iran a kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran da cewa babban laifi ne a kan ‘yan adamtaka.
Tashar Presstv ta bayar da rahoton cewa, a zaman da kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya gudanar a jiya a babban ofishin kwamitin da ke birnin Geneva na kasar Switzerland, Isma’il Baqa’i Hamaneh wakilin Iran a kwamitin, ya bayyana takunkumin da Amurka ta kakaba wa kasarsa da cewa babban laifi ne kan ‘yan adam.
Wakilin na Iran ya ce takunkumin Amurka yana cutar da al’ummar kasar ne kai tsaye domin yin amfani da hakan a matsayin wani makami na siyasa a kan kasar ta Iran, wanda hakan ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa.
A bangare guda kuma Isam’il Baqai’i ya caccaki shugabar kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya, dangane da yadda taki saka takunkumin Amurka a kan Iran a cikin laifuka na cin zarafin ‘yan adam.
Amurka dai tana matsa lamba ne kan Iran domin ta mika mika wuya ga manufofinta a yankin gabas ta tsakiya, lamarin da Iran din taki amincewa da shi.
/129
1 Oktoba 2019 - 04:39
Lambar labari: 979457
Wakilin Iran a kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran da cewa babban laifi ne a kan ‘yan adamtaka.