26 Satumba 2019 - 04:23
Larijani Ya Mayar Da Martani Kan Danganta Iran Da Harin Aramco

Shugaban Majalisar dokokin jamhoriyar musulinci ta Iran ya ce sanarwar da kasashe uku na Turai suka fitar kan kasar Iran ya nuna kiyayarsu a fili kan jamhoriyar musulinci.

(ABNA24.com) Shugaban Majalisar dokokin jamhoriyar musulinci ta Iran ya ce sanarwar da kasashe uku na Turai suka fitar kan kasar Iran ya nuna kiyayarsu a fili kan jamhoriyar musulinci.

A daren litinin din da ta gabata ce kasashen Birtaniya da Faransa da Jamus suka fitar da bayanin hadin gwiwa inda a ciki suka dora alhakin harin da jiragen yaki marasa matuka na kasar Yemen suka kai kan cibiyoyin man fetir na kamfanin Aramco mallakin kasar Saudiya ba tare da su bayyana wani dalili ba.

A ranar 14 ga wannan wata na satumba ne dakarun tsaron kasar Yemen suka kai hari kan ciboyoyin man fetir na kamfanin Aramco mallakin kasar Saudiya da jirage marasa matuki 10, a matsayin mayar da martani kan hare-haren wuce gona da iri da kawancen saudiya ke kaiwa kan al'ummar kasar Yemen.

Shugaban Majalisar dokokin Iran Dakta Ali Larijani ya ce Yamaniyawa da kansu sun ce sune suka kai harin a matsayin mayar da martani , amma abin mamaki wadannan kasashe na zarkin kasar Iran.

Larijani ya ce duk wata kasa da ta kuskure da kawo wa kasar Iran hari, to shakka babu za ta fuskanci martani.

Yayin da yake mayar da martani kan jawabin shugaban Amurka Donal Trump a zauran MDD, Shugaban Majalisar dokokin Iran ya ce Amurkawa sun jarabtu da samun makaryacin shugaban kasa, sannan ya yi ishara kan yadda kasar Amurka ta samar da kungiyoyin 'yan ta'adda a yankin, musaman ma kungiyar ISIS, tare yayin da Shugaba Trump dake bayyana kasar Iran a matsayin kasa dake goyon bayan 'yan ta'adda, Duniya kuma ta shaida cewa jamhoriyar musulinci ta Iran ta taka mahimiyar rawa wajen kawo karshen kungiyoyin 'yan ta'adda a kasashen Siriya da Iraki.



/129