(ABNA24.com) Lauwan tsohon shugaban kasar na Tunisiya, Munir Bin Saliha ya shaida wa kamfanin dillancin labarun Jamus ( DPI) cewa; Tsohon shugaban kasar ta Tunisiya ya mutu ne a yau Alhamis a birnin Jiddah.
Tun makwanni biyu da su ka gabata ne dai aka kai Bin Ali zuwa asibiti domin duba lafiyarsa da ta tabarbare.
A shekarar 2011 ne dai Bin Ali ya fice daga kasarsa Tunisiya zuwa kasar Saudiyya domin neman mafaka, bayan da al’ummar kasar su ka yi masa bore.
Ya mulki kasar Tunisiya na tsawon shekaru 23, ya kuma mutu yana da shekaru 83.
/129
21 Satumba 2019 - 06:54
Lambar labari: 976976
Lauwan tsohon shugaban kasar na Tunisiya, Munir Bin Saliha ya shaida wa kamfanin dillancin labarun Jamus ( DPI) cewa; Tsohon shugaban kasar ta Tunisiya ya mutu ne a yau Alhamis a birnin Jiddah.