(ABNA24.com) Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta ce; dole ne gwamnatin Al saud da abokan kawancenta da suke kashe al’ummar Yemen su dandanta kuda kan abin da suke aikatawa.
A lokacin da yake zantawa da manema labarai jiyaa birnin San’a fadar mulkin kasar Yemen, Muhammad Abdussalam kusa a kungiyar Ansallah da aka fi sani da Alhuthi ya bayyana hare-haren da suka kaddamar kan wuraren sarrafa albarkatun mai na kasar Saudiyya da cewa hakkinsu ne su yi ramuwar gayya kan abin da ake yi musu, kuma a musulunci haka bai saba ba.
Ya ce har yanzu ba su rama ko da kashi daya cikin dari na barnar da Saudiyya ta yi musu ba, domin kuwa matatar mai bat a kai darajar ran mutum daya ba, balantana dubban fararen hula da Saudiyya ta kashe a kasar Yemen a cikin shekaru da takwashe tana kaddamar da hari kan kasar, tare da taimakon Amurka da wasu kasashen turai gami da Isra’ila.
Haka nan kuma ya yi ishara da cewa, wadannan hare-hare da suka kaddamar kan kamfanin aramco somin tabi ne, domin kuwa akwai wasu hare-hare na zuwa, matukar dai Al Saud ba su kawo karshen kisan kiyashin da suke yi kan al’ummar kasar Yemen ba.
/129
18 Satumba 2019 - 05:38
Lambar labari: 976453
Kungiyar Ansarallah ta kasar Yemen ta ce; dole ne gwamnatin Al saud da abokan kawancenta da suke kashe al’ummar Yemen su dandanta kuda kan abin da suke aikatawa.