(ABNA24.com) Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana dangantaka tsakanin kasar Iran da Rasha tana da karfi sosai kuma yakamata kasashen biyu su kara karfafata.
Tashar talabijin ta Al-Alam wacce take watsa shirye shiryenta a nan birnin Tehran ta nakalto shugaban Ruhani yana fadar haka a gefen taron kasashe ukku , wato Iran, Turkiya da kuma Rasha dangane da rikicin kasar Siriya a birnin Ankara babban birnin kasar Turkiya a jiya Litinin.
Shugaban ya kara da cewa banda dangantaka ta manya-manyan kungiyoyin kasa da kasa ta suka hada kasashen biyu, kamar MDD, kungiyar Shanhai da sauransu, Iran tana mu’amala da kasar Rasha kan fasahar Nukliya da kuma harkar kasuwanci kai tsaye da kudaden kasashensu ba tare da shiga tsakani na kudaden wasu kasashen ba.
A wani bangaren na jawabinsa a ganawar shuwagabannin biyu, shugaban Ruhani ya bayyana cewa samuwar sojojin kasar Amurka a kasar Siriya ba tare da yardarm gwamnatin kasar ba yana daga cikin abubuwan da suke hana zaman lafiya a kasar.
/129
17 Satumba 2019 - 09:31
Lambar labari: 976245
Shugaban kasar Iran Dr Hassan Ruhani ya bayyana dangantaka tsakanin kasar Iran da Rasha tana da karfi sosai kuma yakamata kasashen biyu su kara karfafata.