16 Satumba 2026 - 21:39
Source: ABNA24
Bututun Man Saudiyya Ba Ranar Gyara Shi Bayan Kai Masa Hari

Halin Bututun Mai Na Saudiyya Ya Shoga Bayan Harin Yamen Har Yanzu Ba A San Ya Za’a Iya Gayara Shi Ba, Idan Iran Ta Ci Gaba Da Riƙe Mashigar Hormuz Da Ƙarfi Zuwa Wata Ɗaya, Duniya Za Ta Ga Abin Mamaki Da Bata Taba Gani Na.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA – ya ruwaito cewa: Reuters game da halin bututun mai na Saudiyya da aka lalata a hare-haren Yemen ta ruwaito: lokacin gyaran tashoshin turawa mai na 8 da 9 na bututun mai na Saudiyya daga gabas zuwa yamma har yanzu ba a san ya za’ai ba.

A gefe guda kuma ajiyar mai da ake iya amfani da ita a duk faɗin duniya, wanda ta kasance kusan ganga biliyan 8.4 kafin rufe mashigar Hormuz a watan Fabrairu 2026, ta ragu zuwa kusan ganga biliyan 6.8 a wannan watan; bisa ga rahoton sashen bincike na JPMorgan.

Wannan matakin da ake kira "Ƙasan Aiki (Operational Floor)" yana nufin kaiwa ga mafi ƙarancin matakin ajiyar mai wanda a cewar JPMorgan ya zama dole don ci gaba da kulawa da bututu da ci gaba da ayyukan matatun mai a luara da wannan yanayi.

JPMorgan a cikin watanni biyu da suka gabata ta yi gargaɗi cewa idan yaƙin ya ci gaba ba a warware shi ba, ajiyar za ta kai matakin damuwa na aiki a watan Yuni kuma zata kai ga zuwa ƙasan aiki a watan Satumba. Duk hasashen biyu sun tafi daidai da Shirin da ake gudanarwa.

Haka kuma JPMorgan a cikin wannan hoto ta yi hasashen kamar haka.

Cewa ya isa kawai Iran ta ci gaba da riƙe famfon mai na mashigar Hormuz da ƙarfi wata ɗaya, sannan duniya za ta ga abin mamaki dangane da muhimmancin lamarin

…………………  

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha