8 Satumba 2019 - 16:42
Iran: Shugaban Hukumar IAEA Ya Gana Da Zarif A Tehran

Shugaban riko na hukumar makamashin nukiliya ta Duniya ya gana da ministan harakokin wajen Iran a nan birnin Tehran

ABNA: Shugaban riko na hukumar makamashin nukiliya ta Duniya ya gana da ministan harakokin wajen Iran a nan birnin Tehran

Da safiyar yau lahadi ce Cornel Feruta shugaban riko na hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya ya isa birnin Tehran da nufin ganawa da hukumomin birnin Tehran.

Bayan ganawarsa da shugaban hukumar kula da makmashin nukiliya ta kasar Iran Ali Akbar Salihi, mista Cornel Faruta ya gana da ministan harakokin wajen Iran Muhamad javad Zarif.

A yayin ganawartasu, ministan harakokin wajen Iran ya bayyana cewa yarjejejeniyar nukiliyar da kasar Iran ta cimma da manyan kasashen Duniya a shekarar 2015, yarjejeniyar da ya kamata dukkanin bangarorin biyu su yi aiki da ita, idan bangare guda yaki aiki da ita, to jamhoriyar musulinci ta Iran nada hakin daukan mataki kuma a lokacin da ya dace kamar yadda ta dauka na jingine wani bangare na yarjejeniyar a mataki na uku.

A ranar 8 ga watan Mayun shekarar 2018 ne kasar Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliya da kasar Iran din ta cimma da manyan kasashe biyar na Duniya gami da kasar Jamus a shekarar 2015.

Bayan hakuri na shekara guda, jamhoriyar musulinci ta Iran din ta dauki matakin jingine wani bangare na yarjejeniya bisa doka mai lamba 26 da 36 na yarjejeniyar.

A halin da ake ciki kasar ta Iran ta jingine yarjejeniyar takaita tace sinadirin Uranium dinta daga kashi 3.67, sannan kuma ta jingine yarjejeniyar takaita bincike da kuma bunkasa sinadarin karfen Uranium kamar yadda aka cimma a yarjejeniyar ta 2015.

................

300