27 Agusta 2019 - 10:09
Kasar Sin Ta Jaddada Aniyarta Ta Kara Fadada Dangantakarta Da Kasar Iran

Wannan yana zuwa ne a lokacin ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iran Jawad Zarif ya kai zuwa kasar Sin inda ya gana da shugaban kasar da wasu manyan mukarrraban gwamnati.

(ABNA24.com)  Wannan yana zuwa ne a lokacin ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Iran Jawad Zarif ya kai zuwa kasar Sin inda ya gana da shugaban kasar da wasu manyan mukarrraban gwamnati.A lokacin ganawar tasu ministan harkokin wajen kasar China Wank Yi ya bayyana cewa: kasarsa tana goyon bayan duk wani koari game da kare yarjejeniyar da aka cimma kan shirin nukiliyar Kasar Iran ta ko wane bangare .

Ana shi bangaren jawad Zarfi ya bayyana cewa a halin yanzu yanayin yadda wasu kasashe ke take dokokin kasa da kasa yana barazana ga sulhu da zaman lafiyan duniya, don haka Iran tana adawa da duk wani shiga sharo ba sha nu a harkokin cikin gidan wata kasa, ya kara da cewa: Iran a shirye take ta kara karfafa dangantakarta tsakaninta da kasar Sin a bangarorin siyasa,tattalin arzki,kimiya da fasaha,tare da yin aiki tare domin ciyar da tattalin arzikin kasashen gaba.
Daga karshe ana saran ministan harkokin wajen na kasar Iran zai isa kasar Japan bayan kammala ziyarar kwanaki biyu a kasar ta China.


/129