(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran Faransa ya nakalto mazauna kauyen na cewa maharan sun kai harin ne cikin daren Juma'ar da ta gabata a gundumar Gueskerou da ke yankin Diffa, yankin kuma da ke fama da hare-hare da kuma garkuwa da mutane.
Shaidu sun bayyaba cewa 11 daga cikin wadanda suka mutun, an kashe su ne ta hanyar harbi da bindiga.
Ko cikin watan Maris da ya gabata ma an kai irin wannan harin wanda ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula takwas da kuma jami'an 'yan sanda bakwai a kauyen.
A nasa bangare, magajin Garin Gueskerou Hussaini Boucary ya shaida wa 'yan jarida cewa; an binne wadanda suka rasa rayukan nasu da safiyar jiya Asabar.
Wannan harin na zuwa ne kwana biyu kacal bayan kai wani makamancinsa a garuruwan Konduga da Gubio da Magumeri na jihar Borno dake arewacin Najeriya.
Tuni dai mayakan Boko Haram ne wadanda ke biyayya ga kungiyar IS wato ISWAP suka dauki alhakin kai harin.
/129
26 Agusta 2019 - 09:00
Lambar labari: 971754
Mayakan kungiyar boko haram sun kashe mutanea wani kauye da ke kudu maso gabashin jamhuriyar Nijar