26 Agusta 2019 - 09:00
Kungiyar G7 Ta Bukaci Macron Da Ya Isar Da Sakonta Zuwa Ga Kasar Iran

Kasashen bakwai masu karfin tattalin arziki a Duniya dake gudanar da taronsu a Faransa sun dora wa shugaban kasar ta Faransa Emanuel Macron nauyin isar da sakonsu da kuma tattaunawa da kasar Iran.

(ABNA24.com) Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto majiyar fadar shugaban kasar Faransa na cewa Shugabanin kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a Duniya dake gudanar da taronsu a kudu maso yammacin kasar Faransa sun cimma matsaya kan wakilta Shugaba Macron ya tattauna da kasar Iran a madadinsu da kuma isar da sakonsu ga shugabanin kasar ta Iran.

Majiyar tayi ikirarin cewa sakon na kungiyar G7 ya fi mayar da hankali ne kan yadda za a hana kasar Iran din ta mallaki makaman nukiliya da kuma kawo karshen damuwar da ake da ita da tekun Fasha.

Tun a jiya Asabar ne kasashen bakwai masu karfin tattalin arziki na Duniya da suka hada da Amurka, Birtaniya, Jamus, Italiya da Canada da Japan gami da mai masaukin bakin wato Faransa suka fara taronsu karo na 45 a birnin Biarritz dake kudu maso yammacin kasar.

Kafin hakan dai, a ranar Juma'ar da ta gabata, ministan harakokin wajen jamhuriyar musulunci ta Iran Muhamad Zavad Zarif ya ziyarci kasar ta Faransa, inda ya gana da hukumomin kasar ciki kuwa har da shugaba Macron inda ya jaddada masa cewa idan har ana so kasarsa ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015, to dole ne kasashen na Turai su cika alkawarin da suka dauka na aiki da yarjejeniyar bayan ficewar kasar Amurka daga cikinta.




/129