24 Agusta 2019 - 08:06
Rikice-Rikice Sun Tilasta Rufe Makarantu 9000 A Kasashen Yammaci Da Tsakiyar Afrika

A wani rahoto da hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta fitar ya nuna cewa kimanin makerantu dubu tara ne aka rufe da hakan ya tilastawa sama da yara miliyan daya da dubu dari tara barin

(ABNA24.com) A wani rahoto da hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya UNICEF ta fitar ya nuna cewa kimanin makerantu dubu tara ne aka rufe da hakan ya tilastawa sama da yara miliyan daya da dubu dari tara barin makarantunsaboda yawan karuwar tashe tashen hankula a yankin yammaci da ta tsakiyar afrika ,inda ake kai hare hare kan makarantu da wuraren bayar da ilimi,

A wani hari da aka kai a kasashen Mali, Borkina Faso, da kasar Niger inda masu tsatsauran ra’ayin addini suke da karfi, sun zafafakai hare haren a yan shekaru biyun da suka gabata da hakan ya jaworufe makarantu, mafi yawancin rikicin dake faruwa a yankin makarantu da cibiyoyin bada Ilimi na daga cikin wuraren da rikicin yafi shafa, saboda kyamar karatun boko da suke yi,

Hari ila yau Rahoton ya ci gaba da cewa a irin wadannanyankunan rikici na hana yaya mata zuwa makaranta, sai dai duk da wannan rikicin makaranta ta kasance wurine da yara suke zuwa domin samun farinciki da koyon sabon abusama da makarantu 2000 ne aka rufesu a kasar Borkina Faso da kuma guda 900 a kasar Mali sakamkon karuwar tashin hankali da ake samu a kasashen a cewa hukumar Unicef



/129