22 Agusta 2019 - 08:40
Jawabin Jagora A Ga Jamian Gwamnatin Kasar Iran

Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’I, a jawabin da ya yiwa shugaban kasa da majalisar ministocinsa a jiya Laraba, a dai-dai lokacinda aka shiga makon gwamnati, ya bayyana ginshikai guda ukku wadanda yakamata shugaban kasa da majalisar ministocinsa su bada karfi a kansu don kyautata tattalin arzikin kasar.

(ABNA24.com) Jagoran juyin juya halin musulunci Ayatullahi Sayyeed Aliyul Khamina’I, a jawabin da ya yiwa shugaban kasa da majalisar ministocinsa a jiya Laraba, a dai-dai lokacinda aka shiga makon gwamnati, ya bayyana ginshikai guda ukku wadanda yakamata shugaban kasa da majalisar ministocinsa su bada karfi a kansu don kyautata tattalin arzikin kasar.

Abubuwa guda ukku wanda jagoran ya ambata sun hada da dakatar da dogaro da danyen man fetur a matsayin hanyar samun kudaden shiga na gwamnatin kasar, maid a hankali kan ayyukan raya tattalin narziki wadanda zau bunkasa wasu bangarori, sanna da sauya irin kallon da akewa jami’an gwamnati takewa masu masana’antu a kasar

Dangane da bangaren farko, jagoran ya ce: na sha nanatawa kan cewa, gwamnati zata iya amfani dam asana kwararru da masu masana’antu wajen samarda albarkatun iskar gasa da man fetur, wadanda ba danayen man fetur ba wajen bunkata tattalin arzikinkasa wanda bai dogara a kan danyen man fetur ba, abinda za’a sami na kudaden shiga a irin wadanan kayayyaki zasu fi abinda danyen man fetur zai samar na kudaden shiga.

Dangane da “tattalin arziki mai juriya” kuma jagoran ya bayyana cewa : Tattalin arziki mai juriya shi ne tattalin arzikinda zai iya jurewa makirce-makircen makiya ko wani iri ne, sannan kuma zai tabbatar da tattalin arziki wanda baya girgiza kuma wanda ba zai cutu sosai ba idan ya gaba da matsalolin da makiya suke samarwa don rusa shi.

Jagoran ya kara da cewa duk tare ayyuka masu yawa da aka yi ya zuwa yanzu a wannan bangaren, amma har yanzu akwai ayyuka masu yawa da yakamata a yi don rage ko kuma kawo karshen dogaro da danyen man fetur a matsayin hanyar samar da kudade ga gwamnati. Shi kuma ya sa har yanzun, tattalin arzikin yake cutuwa idan makay suka kirkiro masa matsaloli.

Jagoran har’ila yau ya kara da cewa,wannan matsalar ce tasa, a duk lokacinda wasu kasashe suke son cutar da tattalin arzikin kasarmu, suke dorawa kamfanonin sarrafawa kayakin da ba’a sarrafasu ba.

Ya ce a cikin “muradummu na shekaru 20 da suka gabata” akwai batun cewa samun ci gaba na a zo a gani a cikin kasarmu zai samu ne kawai idan mun sami ilmin da fasaha mai zurfi na sarrafa kayakin da ba’a sarrafa su ba. Kamar man fetur da gas, da kayakin noma da kuma ma’adinai daban-daban da muke da su a cikin kasa.

A wani bangare na jawabinsa jagoran ya bayyana cewa, a cikin yakin tattalin arziki da muka shiga da manya-manyan kasashen duniya, yin nesa daga tattalin arziki mai dogaro da sayar da danyen man fetur yana da muhimmanci a cikin nasarorin da zamu samu a gaban makiya. Sannan yakamata ku gane kan cewa karfin tattalin arziki shi ne ginshikin wanzuwar jumhuriyar musulunci a Iran.

Ya ce, saboda dan ci gaban da muka samu a cikin shekaru 40 da suka gabata, shi yasa makiyammu ba zasu iya yin kome da mu ba, sannan da yar dar Allah a cikin wasu shekaru 40 na gaba ma ba zasu iya yin kome ba.

Daga karshe jagoran ya kammala da cewa karfin tattalin arziki wanda ya dogara da masana’antu na cikin gida, da kuma fasahar masana a cikin gida shi ne garkuwammu kuma maganin duk shishigin da makiya zasu iyi mana a nan gaba.



/129