4 Oktoba 2026 - 20:20
Source: ABNA24
Ƙwarewar Jagora Ayatullah Sayyid Mojtaba Khamenei Kan Batutuwan Soji Da Tsaro

Tushen ayyukan leƙen asiri, tsaro da soji, ako yaushe suna cikin ɓoyewa da asirtawa ne; amma wani lokaci girma da yawan ayyukan mutum a waɗannan batutuwa, yakan bayyana har wasu ƙananan sassan waɗannan batutuwan ɓoye su bayyana. Batun da ake iya ganinsa a cikin tafiyar da yanayi Ayatullah Mojtaba Khamenei.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa da Ƙasa na Ahlul-Bayt (AS) – ABNA: A cikin sassan da suka gabata na wannan rubutu, an bayyana batun "hidima ga marasa galihu" a tafiya da yanayi Ayatullah Sayyid Mojtaba Khamenei. A wannan sashe, an bayyana ƙwarewarsa kan batutuwan soji da tsaro.

Tawali'u da ƙoƙarin "kada a gan shi" suna daga cikin siffofin Ayatullah Sayyid Mojtaba Hosseini Khamenei; ta yadda dubban ayyukansa na hauza, hidima, Ilimi da bincike cikin kusan shekaru arba'in da suka gabata, ba su taɓa samun damar bayyanawa a matakin jama'a ba. Waɗannan ci gaba da ƙoƙarin "kada a gan shi," idan aka haɗa su da ƙoƙari kamar ayyukan leƙen asiri, tsaro da soji — waɗanda a zahirinsu suke da tushe na "koyaushe a ɓoye da sirri" ne — ana iya tunanin yadda samun labarinsu zai fi wahala da tsanani.

Ayatullah Sayyid Mojtaba Hosseini Khamenei, cikin kusan shekaru 30 da suka gabata, a matsayin wakili daga shahidin jagoran juyin juya halin Musulunci, sau da yawa ya jagoranci batutuwa daban-daban a fannonin soji da tsaro. Girman ƙwarewarsa kan waɗannan batutuwa ya kai matakin da ya ba wa makusantan mashawartan soji na shahidin jagora mamaki. Misali, Sardar Manjo Janar Rahim Safavi tsohon kwamandan Rundunar IRGC, kuma daga cikin mashawartan soji na shahidin jagora, shekaru da yawa da suka gabata game da wannan siffarsa ya ce: "Mu kwamandojin soji muna cikin wani taro kuma wani bahasi na soji ya taso, Haji Agha Mojtaba ya tashi, ya ba da ra'ayi kuma aka rubuta bayan ra’ayin daya bayar cikin allo sau uku, a nan kwamandojin soji duk sun sunkuya a gaban ra'ayinsa a al'amuran soji, shi a cikkakkiyar ma'ana ya ƙware kan batutuwan soji."

Tsare sirri da takatsantsan suna daga cikin muhimman siffofin hukumomin leƙen asiri; ta yadda sojojin leƙen asiri har ma ga iyalansu ko wasu abokan aiki a wasu sassan wannan ƙungiyar ba a san su ba. Wannan batu, yana sa bayyana matsalolin ciki da waje na kowace ƙungiyar tsaro da neman warware su ya zama mai rikitarwa sosai kuma babu shakka, mai warware waɗannan sabanin dole ya kasance daga cikin mafi kololuwar gudanarwa da amintattun mutane na ƙasar. Cikin shekarun da suka gabata, Ayatullah Mojtaba Khamenei sau da yawa a wasu batutuwan tsaro na musamman na ƙasar, ya kasance mai warware sabanin tsakanin hukumomin tsaro wanda hakan ke nuni da amincewar waɗannan hukumomi ga fifikonsa, ƙwarewarsa da gudanarwarsa kan batutuwan leƙen asiri da tsaro a matakin mafi girma da zai yiwu.

Babu shakka, wannan ikon gudanarwa da babban fifikon tsaro na Ayatullah Sayyid Mojtaba Khamenei ne ya sa shirya don cimma wasu daga cikin ayyukan makamai na soji, waɗanda suka kasance cikin tsari da "cikakken sirri" kuma har ma saboda wasu dalilai bai yiwu an ba da gudanarwarsu ta ofishin soji na ofishin Jagora Mai Girma ba, amma aka ba shi don ya aiwatar da su ta hanyar amfani da mutane masu ilimi da ƙarfin fasaha da kimiyya waɗanda ya san su sosai, amma wasu ba su san su ba.

Wasu daga cikin mutanen da suka shafe fiye da shekaru arba'in suna tare da shi, game da ikon gudanarwarsa sun ce: "Siffarsa ita ce duk wani aiki da aka ba Haji Agha Mojtaba, yana bin diddiginsa da jajircewa har zuwa ƙarshen sakamako, ba ya barin aikin a tsakiyar hanya kuma ba ya sakaci."

A cikin sassan da suka gabata na wannan rubutu, za a nazarci salon zamantakewa da gudanarwa ta Ayatullah Sayyid Mojtaba Khamenei kan batun fagen gwagwarmaya da yunkurin jihadi.

Madogara:

Jawabin Hujjatul-Islam wal-Muslimin Dr. Abdullah Keyvani, wakilin mutanen Chaharmahal da Bakhtiari a majalisar malaman jagoranci

Tattaunawa da Dr. Mehdi Meshki, memba na ƙwararrun malamai na cibiyar Imam Khomeini (Allah ya jikansa)

Sayyid Ali Asghar Hosseini/ Kamfanin Dillancin Labarai na ABNA

_____

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha