3 Agusta 2019 - 06:15
An Bukaci Gudanar da Bincike Kan Harbin Karamin Yaro Da Isra’ila Ta Yi

Bangaren kasa da kasa, kwamitin kare hakkin bil adama na MDD ya bukaci a gudanar da bicike kan harbin wani yaro da sojojin Isra’ila suka yi.

(ABNA24.com) Bangaren kasa da kasa, kwamitin kare hakkin bil adama na MDD ya bukaci a gudanar da bicike kan harbin wani yaro da sojojin Isra’ila suka yi.

Shugaban kwamitin kare hakkin bil adama na majalisar dinkin duniya ya bayyana damuwa kan halin da Abdulrahman Al-shawi yak e ciki.

Ya ce wannan dan shekaru 9 da haihuwa baya a matsayin wata barazana ga Isra’la, amma jami’an tsaro sun harbe shi da harsasai masu rai a garin Nablus.

Jami’in y ce suna bukatar ganin an gudanar da bincike na gaskiya kana bin da ya faru da wannan yaro, kuma a dauki matakai na hukunta wadanda suka aikata hakan.

A jiya ce sojojin Isra’ila suka bude wuta kan wannan karamin yaroa  garin Nablus a lokacin da wasu matasa suke wani jerin gwanoa  lokacin da yke tsayea  gefen titi, a halin yanzu yana nan rai kwakwai mutu kwakwai.



/129