29 Yuli 2019 - 04:03
Ministocin Harkokin Wajen Iran Da Oman Sun Gana A Tehran

Muhammad Jawad Zareef ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da tokoransa na kasar Omman a yau asabar a nan birnin Tehran.

(ABNA24.com) Muhammad Jawad Zareef ministan harkokin wajen kasar Iran ya gana da tokoransa na kasar Omman a yau asabar a nan birnin Tehran.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa wannan shi ne karo na biyu kenan, wanda Yusuf bin Alawi ministan harkokin wajen kasar Omman yake ganawa da jami’an gwamnatin kasar Iran, inda suke tattauna batun dangantakar kasashen biyu da kuma matsalolin yankin Asia ta yamma.

A cikin watan Mayun da ya gabata ne, Alawi ya ziyarci kasar ta Iran ta karshe, sai kuma bayan haka, mataimakin ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Araqci ya ziyarci birnin Muskat babban birnin kasar ta Omman, amma ya musanta cewa ziyararsa na da dangantaka da batun sassauta matsalolin da ke tsakanin Iran da Amurka ba.

Sau da dama gwamnatin kasar Oman takan zama mai isar da sakon gwamnatocin Amurka ga Tehran.



/129