(ABNA24.com) A Mali, akalla mutane, shida ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu, sakamakon matsalar karamcin abinci mai gina jiki a tsakiyar kasar mai fama da matsalar tsaro.
Matsalar tsaro da ake fama da ita a tsakiyar wannan kasar ta Mali, na hana isar da kayan abinci a cewar wasu majiyoyin gwamnati dana kananan hukumomin yankunan jihar.
da yake sanar da hakan ga kamfanin dilancin labaren AFP, mukadashin magajin karamar hukumar Mondoro dake jihar ta Mopti, ya an samu mutuwar mutane shida a kauyen Tiguila.
Ita ma nata bangare ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar ta tabbatar da labarin.
Bayanai sun nuna cewa a bana, an yi rejistan mutane 100 da matsalar karamcin abinci ta shafa a cikin kauyuka 25 na tsakiyar kasar.
/129
25 Yuli 2019 - 07:06
Lambar labari: 964370
A Mali, akalla mutane, shida ne aka rawaito cewa sun rasa rayukansu, sakamakon matsalar karamcin abinci mai gina jiki a tsakiyar kasar mai fama da matsalar tsaro.