(ABNA24.com) Hukumomin Iran, sun sanar da cewa, kasar Saudiyya, ta sallami wani jirgin dakon man fetur dinsu da take rike da tun a ranar 30 ga watan Afrilu na wannan shekara.
Tuni jirgin dakon man « Happiness 1 », ya kama hanyarsa ta zuwa Iran, kamar yadda ministan kula da hanyoyi da bunkasa birane na kasar ya sanar.
Jirgin wanda mallakin kamfanin man fetur na Iran ne, ana rike da shi ne a tashar ruwan Djeddah, ta Saudiyya, bayan daya samu matsala inji, amma daga bisani sojojin na Saudiyya suka tsare shi.
Iran ta sanar da cewa da jirgin da dukkan mambobinsa, sun riga sun kama hanyar shiga ruwan Jamhuriya musulinci ta Iran.
An dai sallami jirgin dakon man na Iran ne, bisa tattaunawa ta masu ruwa da tsaki ta tsakanin kasashen biyu.
/129
23 Yuli 2019 - 04:33
Lambar labari: 963592
Hukumomin Iran, sun sanar da cewa, kasar Saudiyya, ta sallami wani jirgin dakon man fetur dinsu da take rike da tun a ranar 30 ga watan Afrilu na wannan shekara.