(ABNA24.com) Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto mataimakin ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Yabkov yana cewa dalilan da kasar Iran ta bayyana na tsare jirgin ruwan kasar Britania mai suna “Stena Impero” sun fi zama gaskiya, idan an kwatanta da dalilan da gwamnatin Britania ta bayar na kwace jirgin ruwan kasar Iran mai suna Grace 1 a kusa da jabal Tariq na kasar Espaniya.
A ranar 19 ga watan yuli da muke ciki ne dakarun juyin juya halin musukunci a nan Iran suka kwace jirgen ruwan kasar Britaniya a mashigar ruwa ta Hurmuz bayan da jirgin ya aikata laifuffuka da suka sabawa dokokin tukin jiragen ruwa na kasa da kasa, daga ciki, jirgin ya kashe na’uran GPS na shi wanda zai sa a gano inda yake.
A yau litinin ce ake saran firai ministan kasar ta Britania Theresa May zata gudanar da taron gaggawa kan tsare jirnin ruwan, sannan ana ganin shi ne aikinta na karshe a matsayin firai ministan kasar, don zata sauka daga mukaminta a ranar laraba mai zuwa.
/129
23 Yuli 2019 - 04:20
Lambar labari: 963581
Gwamnatin kasar Rasha ta bayyana goyon bayanta ga kasar Iran dangane da tsare jirgin ruwan kasar Britaniya da tayi.