30 Yuni 2019 - 09:43
Halin Da Sheikh Zakzaky Yake Ciki Da Cewa Yana Da Hadari

Harkar muslunci a Najeriya ta bayyana halin da sheikh Ibrahim Zakzaky yake ciki da cewa yana da matukar hadari.

(ABNA24.com) Harkar muslunci a Najeriya ta bayyana halin da sheikh Ibrahim Zakzaky yake ciki da cewa yana da matukar hadari.

A cikin bayanin da ta fitar, Harkar musulunci ta bayyana cewa a sakamakon gwaje-gwajen da likitoci suka gudanar bayan dibar jinin sheikh Zakzaky, an gano cewa akwai sanadaran lead, da candimum a cikin jininsa mai tarin yawa.

Bayanin ya ce likitocin sun tabbatar da cewa irin wanna yanayi yana da matukar hadari, kuma idan ba a gaggauta daukar mataki na tunkarar lamarin ba, to rayuwarsa tana cikin hatsari.

A cikin ‘yan watannin da suka gabata ne dai wata tawagar likitoci daga kwamitin kare hakkokin musulmi na kasar Birtaniya suka ziyarci Sheikh zakzaky, sun kuma bukaci da a bayar da damar fitar da shi domin yi masa magani.

Magoya bayan Harkar Muslucni a Najeriya suna gudanar da jerin gwano da gangamiabirnin Abuja da wasu biranan kasar, domin yin kira ga mahukunta domin su saki Sheikh Zakzaky tare da mai dakinsa domin duba lafiyarsu.


/129