11 Mayu 2019 - 14:49
Nigeria ZataGina Sabuwar Tashar Jirgin Ruwa A Ibadan

Shugaban hukumar gina tashoshin jaragen kasa na kasar China ne ya bayyana haka a jiya Jumma’a a lokacinda ya gana da shugaba Muhammadu Buhari a fadarsa a Abuja.

Mr Fenjian Chen, wanda ya jagoranci wata tawagar manya-manyan mutanen kasar ta Cana zuwa fadar shugaban kasa a jiya Jumma’a ya bayyana cewa kamfaninsa na “China Railway Construction Corporation Limited (CRCC) yana aiki a kasashe 124 a duniya kuma yana da ma’aikata yan Najeriya kadai dubu 18 a halin yanzu.

Mr Chen ya kara da cewa a halin yanzu kamfaninsa yana ayyukan gina layukan dogo da tashoshinsu, tashar jiragen ruwa na kan tudu, gina tituna da kuma samar da kasuwannin na ba kudin fito wato “Free Trade zone”.

Banda haka shugaban kamfanin CRCC ya ce yana saran kamfanin nasa zai samar da ayyuka kimani dubu 40 a ayukan da ke gabansa a halin yanzu.

A nashi bangaren shugaba Muhammadu Buhari ya yabawa kasar China da gudumawar da take bayarwa na tada komatsan tattalin arzikin tarayyar Najeriya, ya kuma yi alkawarin bawa kasar ta Cana tallafin da ya dace don ganin ta gudanar da ayyukanta a cikin kasar ba tare da wata matsala ba.