6 Mayu 2019 - 17:09
Nijar: Mutane da dama sun hallaka a hadarin tankar mai

Rayukan mutane akalla 55 sun salwanta, wasu 36 kuma suka jikkata a Jamhuriyar Nijar cikin daren jiya, sakamakon faduwar wata tankar mai a babban birnin kasar Yamai.

Shaidun gani da ido sun ce mutanen sun gamu da ajalinsu ne a dalilin bindigar da tankar man ta yi, a dai dai lokacin da dandazon jama’a suka garzaya wurin da tankar ta fadi domin dibar man da ke malalewa a kasa.

Bayaga hallaka mutanen da kuma jikkata da dama, fashewar tankar man ya haddasa konewar gidaje da dama, da kuma babura hawa masu yawa da ke kusa da wurin da hadarin ya auku akan titin jirgin kasa da ke hanyar zuwa filin jiragen sama na birnin Yamai.

Gwamnatin Nijar ta dade tana kokarin yakar fasa kwaurin man fetur daga makwabciyarta Najeriya, kasar da itama ta sha fama da fuskantar hadurran bindigar tankokin mai a mafi akasarin lokutan da suke faduwa.