A Jiya Talata da marece ne babban sakataren ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ya sanar da sakin Zainab.
Bugu da kariya ce; Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa Zainab ba ta da laifi ko kadan akan abin da ake zarginta da shi na shigar da kwaya a cikin kasar.
An yi zargin cewa an yi wa Zainab cushen muggan kwayoyi ne a cikin kayanta, tahanyar amfani da sunanta wajen shigar da kwayar cikin kasar Saudiyya.
A jiya Talata ma daian gudanar da Zanga-zanga a bakin ginin karamin ofishin jakadancin Saudiyya dake birnin Kano domin neman a saki Zainab.
Sakamakon zanga-zanga da kiraye-kirayen kungiyoyin kare hakkin bil adama a ciki da wajen Najeriya suka yi ta yi kan batun na Zainab, shugaba Muhammadu Buhari ya ba da umarni ga ma’aikatar shari’ar kasar da ta shiga cikin lamarin, a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta Saidiya ke shirin sare mata kai.