Bayanin wanda bangaren yada labarai na fadar shugaban kasa ya fitar, ya bayyana cewa Buhari zai kaddamar da wasu ayyuka a yau a jihar Borno, da suka hada da ayyukan bunkasa ci gaba ilimi da kiwon lafiya, kafin daga bisani kuma ya kama hanyar London.
Sai dai sanarwar ba ta bayyana hakikanin abin da zai kai shugaban kasar Birtaniya ba, amma an bayyana cewa zai ci gaba da kasancewaacan har zuwa ranar 5 ga watan Mayu mai kamawa.
A cikin shekara ta 2017 dai shugaba Buhari ya yi fama da jinyaabirnin London na kasar Birtaniya lokaci zuwa lokaci, mafi jimawa daga ciki shi ne wanda ya kwashe kwanaki fiye da 100 ana kula da lafiyarsa.
A jiya Laraba ma shugaba Buhari ya kaddamar da wasu ayyuka a jihar Legas,awata ziyarar aiki da ya kai a jihar.