23 Maris 2019 - 18:19
An Kai Wasu Munanan Hare Hare A Kasar Somalia

Rahotanni daga kasar Somalia na cewa a yau an kai wasu munanan hare-hare a cikin birnin Mugadisho fadar mulkin kasar.

Kamfanin dilalncin labaran Reuters ya bayar da rahoton cewa, an kaddamar da wasu munan hare-hare a yau a cikin birnin Mugadisho, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 5 da suka hada har da wani mataimakin minista.

Rahoton ya ce bayan kai harin da bama-bamai, an kuma ji karar harbe-harbe da manyan bindigogi, kuma harin ya auku n a kusa da bababn ginin ma'aikatar ayyuka ta kasar, kamar yadda a a wurin akwai wasu gine-gine  na gwamnati.

wadanda suka ganewa idanaunsu bin da ya faru suna cewa harin ya yi muni matuka, kuma akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasu sakamakon harin ya ci gaba da karuwa.

Tuni dai mahukuntan kasar suka zargi kungiyar Al-shabab da hannua  cikin harin.