Zarif ya ce irin rawar da Amurka take takawa a yankin gabas ta tsakiya ba maslaha ce ga al’ummomin yankin ba, domin kuwa in ban da yake-yake da rikice-rikice na siyasa da bangaranci babu abin da take haddasawa a yankin, abin ban takaici kuma shi ne wasu kasashe sun fada cikin tarkon da Amurka ta dana musu.
Haka nan kuma ya yi ishara da taron da Amurka ta shirya a kwanakin baya a kasar Poland domin nuna kiyayya ga kasar ta Iran, inda Zarif ya ce taron bai yi nasara ba, domin kuwa da dama daga cikin wadanda aka gayyata ba su halarta ba.
Baya ga haka kuma Zarif ya bayyana cewa, yin shiru kan fitintinu da Isra’ila take haifarwa a gabas ta tsakiya da wasu daga cikin masu kirkiro kungiyoyin ‘yan ta’adda da daukar nauyinsu a gabas ta tsakiya, na daya daga cikin abin da ya rusa taron na Poland.