19 Janairu 2019 - 20:25
Kotun Amurka Ta Ce An Kama Marzieh Hashemi Ne Domin Ta Bayar Da Sheda

Wata kotun kasar Amurka a birnin Washington ta bayyana cewa, an kama 'yar jaridar nan mai aiki da tashar Presstv ta kasar Iran ne saboda ta bayar da wata sheda kan wani batu.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, bayanin da kotun ta bayar shi ne cewa, an kama Marzieh Hashemi ne ba domin ta aikata wani lafi ba, domin kuwa babu wani laifi da ake zarginta da aikatawa, amma akwai wani batu wanda ake son ta bayar da sheda a kansa.

Kotun dai ba ta yi wani karin bayani kan abin da ake son marzieh ta bayar da sheda akansa ba, amma dai kotun ta ce da zaran an gama jin ta bakinta dangane da shedar da ake son ta bayar, to za a sallame ta.

Tun a ranar Litinin da ta gabata ce jami'an tsaro na hukumar FBI suka kama ta kuma sun tafi da ita, kuma ba su sanar da iyalanta da danginta ba sai ranar Laraba da ta gabata.

A lokacin da suka kamata dai sun sanya mata ankwa a hannu da kafafunta, kamar yadda kuma suka cire mata lullubinta na musulunci da ke kanta, kamar yadda kuma suka hana cin abinci na halal, inda suka kawo mata naman alade a matsayin abincin da za ta ci, abin da taki yarda da shi.