4 Janairu 2019 - 19:16
An Kashe Dubban Yan Ta'adda A Kasar Siriya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Rasha ta bada sanarwan cewa sojojin kasar sun kashe dubban yan ta'adda a yakin da ta shiga da su a kasar Siriya.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ma'aikatar tsaron kasar Rasha tana fadar haka a jiya Alhamis ta kuma kara da cewa tun lokacinda sojojin kasar Rasha suka fara yakar yan ta'adda a kasar Siriya sun kashe mayaka dubu 87, wadanda 830 daga cikinsu kwamnadojisu ne. Banda haka sojojin kasar Rasha sun wargaba sansanonin mayakan yan ta'adda dubu guda, sannan sun lalata runbunan ajiye makamai da makamashi na yan ta'adda kimani dubu 10.

Rahoton ma'akatar harkokin wajen kasar ta Rasha ya kara da cewa sojojin kasar sun lalata tankunan yaki 650 da kuma motocin yaki 700 a cikin wannan lokacin.

An fara tashe-tashen hankula a kasar Siriya ne a cikin watan Maris na shekara ta 2011, a lokacinda gwamnatin kasar Saudia ta kawayenta na kasashen larabwa da kuma kasashen yamma suka budewa kungiyoyin yan ta'adda kofofin shiga kasar Syriya da Iraqi da nufin kifar da gwamnatocin kasashen biyu, da kuma sake tsarin yankin gabas ta tsakiya, ta yadda babu wata kasa da zata fi HKI karfi a yankin.

Sai dai shigar kasar Raha yakin da kuma kasar Iran da kungiyoyin hizbullah da harshdusshabi na kasar Iraqi sun hanasu su kaiwa ga manufofinsu.