Sanarwar da Ma’aikatar Harkokin Cikin Gidan Somalia ta fitar ta ce, Haysom wanda ke wakiltar Babban magatakaddar Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Gutteress, ba zai iya ci gaba da aiki a kasar ba, sakamakon yadda ya gaza boye muradinsa na kashin kansa akan harkokin gudanarwar kasar.
A cewar sanarwar, Haysom ya keta dokokin da Majalisar ta gindaya masa a matsayinsa na babban jami’i.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce, jami’an tsaron Somalia sun kashe masu zanga-zangar 15 tare da tsare kimanin 300.
Gwamnatin Somalia, ta dogara kan samun agaji daga kasashen ketare, yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke ba ta kudade da kayayyakin bayar da horo ga jami’an tsaron kasar da ke yaki da mayakan al-Shebab.