Shugaban kasar ya kara da cewa rasuwar Aya. Hashimi Shahrudi wani babban rashi ne ga al-ummar Iran da kuma iyalansa, har'ila da kuma makarantun addinin a nan JMI.
Ruhani ya ce Aya. ya bar ayyukan na alkhairi da dama wa al-ummar iran, bayaga daliba da ya karantar shi ne ya kafa Jami'ar Adali da kuma tsarin nan da kyautata dangantaka tsakanin jami'o'i da kuma makarantun ilmin addinin a kasar Iran.
Banda haka Aya Hashimi Shahrudi ya rike mukamin alkalin alkalai na JMI na tsawon shekaru goma, kafin a bashi shugaban majalisar masalar tsarin mulki a nan Iran, mukamin da yake rike da shi har zuwa rasuwarsa a jiya Litinin yana dan shekara 70 a duniya.