9 Satumba 2018 - 16:14
A WURINMU DUK WANDA MANZON ALLAH (SAWA) YA TSINE MASA TSINANNE

Cewar- Sheikh Hamzah Muhammad Lawal

A karatun Al-Milalu Wan Nihal na ranar Juma’a, 3/8/2018, wanda Sheikh Hamzah Muhammad Lawal ya gabatar a makarantarsa dake PRP Unguwan Sanusi Kaduna, malamin ya cigaba da bayanin hadisin Muslim da ire irensa wa’yanda Ahlus Sunnah suke amfani dasu domin bada kariya da sallatar da tsinuwan da Manzon Allah yayi ga wasu mutane a rayuwarsa ta risala. Malamin yace ba wai kawai an kirkiri hadisan bane don kare wa’yanda Annabi ya tsine masu bane kawai, a’a, wasu hadisan an kirkire su ne domin a ci mutumcin Annabi a matsayin daukan fansa da ramuwar gayya kan matakin da Annabi (sawa) ya dauka kan mutane da ake kokarin karewa.
Malamin ya ce;
 “ Duk wanda Manzon Allah (sawa) ya la’anta, to, shi la’ananne ne. Mu a nan muka tsaya. Idan kana so ka zagi Manzon Allah (sawa) kai tsaye ka kasa, to, sai ka zagi Ali (as). Idan shima kana so ka zagi Ali (as) kai tsaye din sai ka kasa, to, sai ka zagi mabiya Ali (as) (sune ‘yan shi’a), ba matsala. Ma’ana, idan Manzon Allah (sawa) ya la’anci wanda baka so ya la’anta, sai ka ga ya kamata ka kuskurantar dashi Annabin ka ce yayi abinda ba daidai ba, sai ka kasa. To, daga karshe in ka ga dama kana iya kuskurantar damu mu, ka ce mu muka yi laifin. Mun yarda mu karbi zomon, ba mu rataya zomon ba da kanmu ba, a rataya mana. Mun yarda mu taka sawon barawon- ba matsala. Mu haka muke. Inda Annabi yake a nan muke.
 “ Duk wanda Manzon Allah (sawa) ya la’anta ya la’anu, wanda duk Manzon Allah (sawa) ya zage shi ya cancanci wannan, wanda duk Manzon Allah (sawa) ya bulale- ba ta’wil- wannan shari’arshi ce (sawa) bulalar, bulalar shari’arshi ce. Wanda duk Manzon Allah (sawa) yayi addu’a a kanshi addu’ar ta tabbata a kanshi. Wannan shine ra’ayinmu, wannan shine mazhabarmu, wannan shine akidarmu, wannan shine addininmu, wannan itace millarmu. Kowa ya gane wannan. Ba ma zagin kowa, ba mu isa mu zagi wani ba, bamu san wanda ya cancanci zagi ko la’ana ba. Idan ya shiga cikin wa’yanda Allah Subhanahu wa Ta’ala yake ce ma; YAL’ANUHUMUL LA’INUN, to, muna daga cikin ALLA’INUL din, mu ne muna daga cikin ALLA’INEEN. Wanda ya fitar da kanshi daga cikin ALLA’INEEN ba matsala- kiri kiri a fahimta. Ba zagin kowa, bama la’antar kowa, ba haka bane yanda ake fadawa mutane. Abinda muke yi shine hikaito Annabi da dabbaqa hukuncin Annabi da kuma rashin karban ta’wili a irin wa’yannan wuraren, da rashin karban izgili ga Annabi a irin wadannan wuraren, da rashin karban daukan fansa da ramuwa a kan Annabi a irin wa’yannan wuraren, da rashin karban cin fuskan Annabi da fuskantanshi da raddi ma Annabi a irin wa’yannan wuraren. Bama yin wa’yannan.  Bama fifita wasu a kan Annabi. Bama kubutar da wasu daga hukuncin Annabi (sawa), sannan bama zaban bangaren wasun Annabi a kan bangaren Annabi. Ba mu suna, wannan ba komai.
 “ Yanzu billahi alaikum duk wani mutum da yake da tajriba yake da gogayya a cikin wannan addinin- bari mu yi tambaya. Duk wani mutum da yake da gogayya a cikin wannan addinin zai iya nuna mana mauridi daya, wuri daya na wani wuri wanda yake Manzon Allah (sawa) ya tsinema wanda bai cancanci tsinuwa ba? Zai yiwu ka kawo mana wuri daya na inda Manzon Allah ya tsinema wanda bai cancanci tsinuwar ba, ko ya bulale wanda bai cancanci bulala ba? Me ka dauki Annabi? Annabi ya tsinema wanda bai cancanci tsinuwa ba? Tsinuwa karamin abu ne? Akwai misali daya da zaka iya kawowa na wani wuri wanda Manzon Allah (sawa) ya zagi wani wanda bai cancanci zagi ba? Zaka iya sheda guda daya na wani mutum daga salihan al’umma wanda Manzon Allah ya tsinemawa- kowane ne wannan- zaka iya kawo mana wannan? Ko zaka iya kawo mana wani wuri wanda Manzon Allah (sawa) ya bulale wani salihin bawa wanda bai cancanci bulala ba? Ko kuma yayi addu’a ta ukuba a kan wani wanda bai cancanci wannan addu’ar ba daga cikin salihan bayin Allah?
 “ Annabi yayi haka! HAASHA ANNABI AL-MAB’US. Nisa da Annabi (sawa) ya zama cewa wannan karyar, wannan kagen ya zama ya jinginu ya zuwa ga Annabinshi. Wai tsinewa wani wanda bai cancanci tsinuwa ba. In har muka yarda wannan kagen, wannan riyawar ta inganta, inda haka zai inganta- ‘IN’ a kan sharadi, mustahil ya inganta, amma an kaddara. Ku kaddara a kan cewa wannan kagen, wannan riyawar zata inganta a kan cewa Annabi yana tsinewa wanda bai cancanta ba, da zai zama Kenan wulakanta da tozarta da rashin nauyi ya gangaro ya shiga zantuka da ayyukan Manzon Allah(sawa). Wannan shine laazim din. Laazim din shine cewa duk abinda Manzon Allah yayi zai zama bai da kima, saboda kila ba daidai bane, kila ya afku ne ba a muhallin shi ba. Kuma a wurinsu Manzon Allah yana yin Magana da ba daidai ba wadda take afkuwa ba a muhallinta ba. Sunce Manzon Allah yana zautuwa, yana kaskantuwa ga sihiri, ana iya sihirce shi, wato a samu saidara a kan tadbirinshi a kan tasarrufinshi yini cikakke, ya zama bai da control, bai da saidara a kan tasarrufofinshi.
 “ Inda a ce wannan kagen ya inganta, to, da shike nan zai zama ba kima a cikin ayyuka da zantukan Manzon Allah (sawa). Haka da irin wannan shakka din ta shiga cikin hukunce hukunce da alkalanci da yake yi da iyakoki da haddodi wanda yake yi. Yace a bulale wani ko yace a yi haddi a kan wani sai ya zama duk ba daidai bane. Da zai zama muna shakka a kan daidai ne ko ba daidai bane, wannan shine lazim din, wannan shine mahzur. Ta yanda mutum ba zai iya gane yanzu ko me Manzon Allah yayi a kan cewa fizguwa ce daga Allah ta sa shi wannan? Koko a’a, yana tunkuduwa ne ya zuwa shahwa, son rai da kuma bice ‘saura’ ta fushi? Ba zaka iya ganewa ba.”