Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) Yace: "Idan na ce abin da suka yi dabbanci ne, na ci zarafin dabba. Ita dabba tana kisa ne ko don tana fuskantar haɗari ko don yunwa, kamar Zaki. Dabbobi ba su kisa saboda kisa. Wannan kisa aka yi saboda kisa. Aka rutsa mu kwanaki uku a jere ana kisa dare da rana. Kisa ne na mugunta. Ana watsa wa mutane fetur ana kona su. "Haka suka yi a Husainiyyah Bakiyyatullah da Gyallesu, suna zubawa mutane mai suna cinna musu wuta, mutane da ransu. Bayan kona mutane da wuta, an bizne mutane da rai.
__ Cikin jawabin Jagora Sayyid braheem Zakzaky (H) a yayin taron tunawa da waki'ar Buhari karo na bakwai.
Shaikh Ibraheem Zakzaky (H): “Muna Yi Wa Juna Ta'aziyya”
—Imam Ibraheem Yaqoub Zakzaky Hafizahullah
"Cikin Hikimar Allah (T), akwai iyayen da suka rasa ƴaƴansu, akwai mutane da yawa da su ka rasa ƴaƴansu. In ya zama ba abinda ya samu nawa ƴaƴan, mutane za su ce "Amma shi ba abinda ya samu nashi iyalan ai." Wannan sai ya zama ya na tausasa musu zukata, tunda dukkan mu abin ya shafe mu. Mu na jin zafin da suke ji, wannan hikimar Allah (T) ce. Dukkanmu abin ya shafe mu, kamar yadda Allah (T) ya ke cewa; Illal lazeena aamanoo wa 'amilus saalihaati wa tawaasaw bilhaqqi wa tawaasaw bissabr. Don haka muna yi wa juna ta'aziyya ne, mu na tausasar juna ne, kuma imaninmu da Allah shi ne ya bamu ikon tahammulin abinda ya faru damu."
—Jagora Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin da yake amsa tambayar yadda ya keji na rashin ƴaƴanshi da Jami'an tsaro suka kashe a Zariya.
Innalillahi Wa'inna Ilaihir Raji'uun.
Wah Musibata.
Allah ka Tsine wa duk wanda yake da Hannu A kan kisan Ƴan'uwanmu...!
21/Jimada Thani/1447
12/12/2025
Your Comment