Osinbajo, wanda ya zama mukaddashin shugaban kasa tun lokacin da shugaban Buhari ya tafi hutun kwana goma a Landan, ne ya bayar da wannan umarnin ta hannun mai taimaka masa na musamman kan harkar yada labarai, Laolu Akande.
Wata sanarwar da Laolu Akande, ya fitar ranar Talata, ta ce an umarnin Lawal Daura ya mika ragamar shugabancin hukumar ga jami'i mafi girma a hukumar ta DSS