Yan lokuta bayan samun kan sa, Shugaban kaar ta Venezuela Nicolas Maduro ya zargi wasu manyan jami’an kasar dake zaune a Amurka da kokarin kifar da gwamnatin sa, Maduro ya kuma zargi Shugaban Colombia Juan Manuel Santos da hannu a harin.
Kasar Venezuela ta fada rikicin siyasa kama daga shekarar da ta 2017, bayan zaben yan majalisu da ga baki daya ake zargi da kasancewa yan amshi shatar Shugaban kasar.
A wannan hari mutane 7 daga cikin mau tsaron Shugaban kasar ne suka samu rauni.
5 Agusta 2018 - 12:22
Lambar labari: 904344
Shugaban kasar Venezuela Nicolas Maduro ya ketare rijaya da baya, bayan da wasu kuramen jirage dauke da bama-bamai suka yi kokarin halaka shi a lokacin da yake jawabi zuwa sojojin kasar a Caracas.