A jiya juma'a ne Birgediya Janar Ridha Talayi Nik ya bayyana haka yana mai kara da cewa; " Amurka da haramtacciyar kasar Isra'ila suna son haifar da rashin tsaro da kuma matsalar tattalin arziki a cikin iyakokin Iran, sai dai za su ci kasa kamar yadda ta kasance da su a cikin shekarun bayan nan a wannan yankin.
Mataimakin ministan tsaron ya ci gaba da cewa; Jamhuriyar musulunci ta Iran ce cibiyar kawancen gwagwarmya a wannan yankin, shi ya sa makiya suke jin haushin jamhuriyar musulunci saboda kashin da su ka sha a cikin kasashen Iraki da Syria da dukkanin yankin gabas ta tsakiya.
Birgediya janar Talayi Nik ya kuma ce; Makamai masu linzamin da Iran take da su za su iya kai hari akan makiya a ko'ina ne cikin gaggawa sannan kuma zai jefa makiyan cikin nadama.
28 Yuli 2018 - 11:23
Lambar labari: 903346
Mataimakin ministan tsaro na Iran ya ce; Iran tana da karfin da za ta iya dakile duk wani makirci na makiya a kowace kusuruwa ta gabas ta tsakiya