Kwamitin shirya zanga zangar a nan Tehran ya bada labarin cewa Malaman addini, da maraji'ai da shuwagabannin yankuna da kuma yan siyasa duk sun bukaci mutanen birnin Tehran su fi don gudanar da wannan zanga-zangar a yau Jumma'a bayan sallar Jumma'a.
Labarin ya kara da cewa fara zanga zangar a wurare 40 a cikin birnin na Tehran, inda masu zanga zangar zasu sake jaddada bai ga jagoran juyin juya halin musulunci kasar da kuma tsarin da ke jagorantar kasar kimani shekaru 40 da suka gabata.
A ranar 28 ga watan Decemban da ta gabata ce wasu masu son tada fitina suka tada tarzoma wanda ya kai ga kate hurumin addini da kuma munana jumhuriyar musulunci . Har'ila yau wanda ya kai ga asarar rayuaka da dukiyoyi.