20 Disamba 2017 - 11:47
A na Tasare Da Yan Najeriya 25,000  A Libiya

Hukumar nan mai yaki da safarar mutane a Najeriyar, watau NAPTIP, ta ce 'yan kasar sama da 25,000 ne ake tsare da su ba bisa ka'ida ba a kasar Libiya.

A rahoton da hukumar ta fitar ta ce bakin hauren ana tsare da su ne tanakar bayi sanan ana sanya su ayukan karfi ko kuma na karuwanci a sansanoni daban a kasar ta Libiya.

Kawo yanzu dai a cewar hukumar 'yan kasar 5,000 ne aka maida da su gida tare da hadin gwiwar hukumar kula da kaurar bakin haure ta MDD, (OIM) da kungiyar tarayya Turai  (UE), kamar yadda shugabar kungiyar Julie Okah-Donli. ta sanar.

Jami'ar ta kara da cewa ya kamata duniya ta baiwa wannan batun mahimmaci sosai.