Daya daga cikin na kusa da Ali Zaydan, Karam Khalid ya shaidawa manema labaru cwa, a ranar talata da dare ne aka sake shi kuma a halin yanzu yana cikin koshin lafiya.
Wata majiyar tace kungiyar da ta yi garkuwa da Zaydan tana da alaka da gwamnatin hadin kan kasa.
Shi dai Ali Zaydan dan shekaru 67 ya rike Pira ministan kasar ta Libya ne daga watan Nuwamba na 2012 ne zuwa Maris na 2015.
Masu adawa da Zaydan suna zaginsa da wawason dukiyar kasar ta Libya a shekarun mulkinsa. An sace shi ne a ranar 13 ga watan nan na Augusta a wani hotel na babban birnin kasar, yayin da ya ke taron manema labaru domin karyata zargn da ake yi masa na satar dukiyar kasa.288