Shugaban hukumar alhazai da kula da harkokin addini a kasar Yamen Abdullahi Amir ya yi tofin Allah tsine kan yadda mahukuntan Saudiyya suke sanya son rai da bakar siyasa a harkokin addinin Musulunci, inda a bana ma mahukuntan na Saudiyya suka sake hana al'ummar Yamen damar zuwa aikin hajji domin sauke farali yau tsawon shekaru uku ke nan a jere.
Har ila yau mahukuntan na Saudiyya sun sanar da aniyarsu ta hana maniyata aikin hajji bana na kasar Siriya zuwa kasar ta Saudiyya domin sauke farali. Haka nan ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhmmad bin Abdur-Rahman Ali Sani ya zargi mahukuntan na Saudiyya da sanya bakar siyasa a harkokin aikin hajji sakamakon barazanar da Saudiyya ta yi na hana maniyata aikin hajjin bana na Qatar zuwa sauke farali.288