Rahotan mai shafi 24 da masana harkar tsaro suka rubutawa kwamitin Sulhu ya ce ana samun wahala wajen gane kudaden da mutane ke aikawa kungiyar a matsayin tallafi.
Rahotan ya ce kungiyar na fadada karfin ta zuwa kudu maso Gabashin Asiya, musamman kudancin Philippines inda yanzu haka aka kashe mutane kusan 700.
Masanan sun bukaci sa ido kan yara da matasa wadanda ake yaudarar su domin sanya su cikin kungiyar.288