Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, masu zanga-zangar biyu sun mutu ne sakamakon harbi da bindiga da 'yan sanda suka yi a kan masu zanga-zangar a yau Laraba a garin Safi.
Wani jami'in 'yan sanda ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa barayi ne suka shiga cikin masu zanga-zangar domin wawushe kayan jama'a, a kan haka suka yi amfani da karfi domin tarwatsa su.
Madugun adawa na kasar Kenya Reila Odinga ya yi watsi da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a jiya a kasar, inda ya zargi Uruhu Kenyatta da hukumar zaben kasar da tafka magudi.288