Kamfanin dillacin labaran Reuters ya ambato wata majiya daga fadar shugaban Najeriya tana cewa Buhari ya fasa dawo wa a karshen mako, sabanin yadda aka yi hasashen zai dawo a ranar Lahadi.
Majiyar ta ce shugaba Buhari ba zai dawo gida ba domin akwai wasu gwaje-gwaje da likitoci za su yi ma sa a yau Litinin.
Ko Yaushe Buhari zai dawo ? wannan ita ce tambayar da ke bakin ‘yan Najeriya.
A watan jiya ne shugaba Buhari ya tafi London domin sake diba lafiyarsa, bayan shafe watanni biyu ba ya Najeriya a tafiyarsa ta watan Janairu.
Har yanzu dai ‘yan Najeriya ba su san irin rashin lafiyar da ke damun shugabansu ba.288