3 Yuni 2017 - 11:41
Sarkin Morocco ba zai halarci taron Ecowas

Sarki Morocco na shida ba zai halarci zaman taro na 51 na kungiyar Ecowas da zai gudana a kasar Liberia daga ranar 3 zuwa 4 ga wannan watan da muke ciki.

Fadar sarki Mohamed na shida ta futar da sanarwa dake zuwa a dai dai lokacin da ake gab da bude zaman taron na yau a birnin Moronvia na kasar ta Liberia.
Kauracewa taron na Ecowas na zuwa ne bayan da Firaministan Isra’ila Benjamin Nethanyahu ya sanar da cewa zai halarci zaman taron .
Ana zaman doya da man ja tsakanin Isra’ila da Morocco, haka zalika wasu kasashen sun sanar da turo wakilan su a taron na Ecowas.288